<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>309</hymn_number>
<title>In Ka Karanta Cikin Matta Fa LW309</title>
<lyrics>[V1]
 1) In ka karanta cikin Matta fa,
 Za ka ga. jawabi, sai mu haskaka
 Muddar muna nan a cikin duniya
 Cetattu na Yesu, mu haskaka.

[V2]
 2) Amma babu dama mu haskaka
 In da wani laifi cikin zuciya.
 Gudu wurin Yesu, roƙi gafara.
 Cetattu na Yesu, mu haskaka.

[V3]
 3) Mutanen da ke kewaye da mu
 Suna duban hali da auyukanmu,
 Kada dai su gani rashin gaskiya.
 Cetattu na Yesu, mu haskaka.

[V4]
 4) Cikin makaranta mu shaida shi,
 Ko a gida kuwa mu hana zunubi.
 Cikin jinin Yesu akwai nasara.
 Cetattu na Yesu, mu haskaka,

[V5]
 5) Cikin ikon Yesu mu bi daidai,
 Dukan aikin duhu sai mu ƙi sosai,
 Mutane dayawa za su gaskata.
 Cetattu na Yesu, mu haskaka.</lyrics>
</song>